An sake samun ce-ce-ku-ce kan tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, bayan da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya zargi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC da hana shi samun kulawar lafiya yayin da yake tsare.
A wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya bayyana cewa El-Rufai ya koka kan matsalar idanuwansa, inda ya ce suna ƙaiƙayi tare da kumburi. A cewarsa, tsohon gwamnan ya nemi a kai shi asibiti domin ƙarin bincike da magani, amma jami'an hukumar sun ƙi amincewa da buƙatar.
Ya ce tun a ranar 4 ga watan Yuni an kai El-Rufai wani asibitin ido domin duba lafiyarsa, amma daga baya yanayin lafiyarsa ya ƙara taɓarɓarewa, lamarin da ya jefa iyalansa cikin damuwa.
Adekeye ya ƙara da cewa jami'an ICPC sun ga halin da idanuwan tsohon gwamnan ke ciki, amma ba su shirya masa wani ƙarin kulawa ta musamman ba. Ya kuma yi zargin cewa an bai wa iyalansa bayanan da ba daidai ba, inda aka ce El-Rufai bai nemi ganin likita ba.
A cewar mai ba shi shawarar, akwai umarnin kotu da ya ba El-Rufai damar samun kulawar lafiya a duk lokacin da ake buƙata, amma ya yi ikirarin cewa ba a aiwatar da wannan umarni yadda ya kamata ba.
Lamarin ya jawo martani daga masu bibiyar harkokin siyasa da shari'a, inda wasu ke kira da a tabbatar da mutunta haƙƙin waɗanda ake tsare da su, musamman idan ya shafi lafiyarsu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ICPC ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye domin mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge ba, yayin da ake ci gaba da jiran matsayinta a hukumance.
Masana harkokin shari'a sun ce idan akwai umarnin kotu da ya tanadi damar samun kulawar lafiya, to ya kamata a tabbatar an aiwatar da shi ba tare da tangarda ba, domin kare haƙƙin wanda ake tsare da shi da kuma tabbatar da bin doka da oda.

0 Comments