An ƙara shiga yanayin fargaba a kasuwannin makamashi na duniya bayan da Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta yi barazanar rufe Mashigar Hormuz gaba ɗaya, wata muhimmiyar hanyar ruwa da ake amfani da ita wajen jigilar man fetur da iskar gas zuwa sassa daban-daban na duniya.
Barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da tsananta a yankin Tekun Fasha, lamarin da ke haifar da damuwa ga ƙasashe da kamfanonin da suka dogara da makamashin da ake fitarwa ta wannan hanya.
IRGC ta bayyana cewa matakin rufe mashigar na iya zama wani martani idan Amurka ta ci gaba da ayyukan da Tehran ke kallon a matsayin tsoma baki da kuma barazana ga tsaron ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta sanar da cewa sojojinta sun kai hari kan wasu cibiyoyin sa ido da ke yankunan Goruk da Qeshm, waɗanda ke ƙarƙashin ikon Iran. A nata ɓangaren, Iran ta ce ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa wasu sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain da Kuwait.
Sai dai rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta ce ta samu nasarar kakkabo makaman ko kuma sun kasa kaiwa wuraren da aka nufa.
Masana harkokin tattalin arziki sun ce duk wani mataki na rufe Mashigar Hormuz zai iya jawo tashin farashin mai a kasuwannin duniya, kasancewar kusan kashi ɗaya cikin huɗu na man fetur da ake safararsa a duniya na bi ta wannan hanya.
Wasu ƙasashen Asiya da Turai da suka dogara sosai kan makamashin Gabas ta Tsakiya sun fara nuna damuwa kan yiwuwar tasirin da rikicin zai yi ga tattalin arzikinsu idan aka samu tangarda ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.
Har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa ɓangarorin biyu za su sassauta matsayinsu, abin da ke ƙara haifar da fargabar cewa rikicin na iya ƙara faɗaɗa tare da shafar kasuwannin makamashi da tsaron yankin baki ɗaya.
Masu sa ido kan al'amuran duniya na ci gaba da kira ga Iran da Amurka da su rungumi tattaunawa da hanyoyin diflomasiyya domin kauce wa wani sabon rikici da zai iya girgiza tattalin arzikin duniya.

0 Comments