An sake bayyana damuwa kan matsalar garkuwa da mutane a arewacin Najeriya bayan da wani bidiyo ya nuna tsohon babban jami’in sojin ƙasar mai ritaya, Manjo Janar Abubakar Rabe, tare da matarsa suna roƙon gwamnati da ta taimaka wajen ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane.
Ma’auratan, waɗanda aka sace a makon da ya gabata yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Katsina, sun bayyana a cikin wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta inda suka yi kira ga hukumomi da shugabannin al’umma da su shiga tsakani domin a samu mafita ga halin da suke ciki.
A cikin bidiyon, matar tsohon janar ɗin ta bayyana cewa masu garkuwar sun gabatar da wasu buƙatu da suka haɗa da sakin wasu mutane uku da suke ikirarin ana tsare da su, tare da mayar musu da wasu dabbobi da suke zargin an ƙwace daga hannunsu.
Ta ce waɗanda ake buƙatar a saki sun haɗa da Sani, Aminu da Nasiru, inda aka ce an kama wasu daga cikinsu a yankuna daban-daban na jihohin Katsina da Kano.
Hajiya Amina Abubakar ta roƙi gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi da su yi duk mai yiwuwa domin ganin an cika waɗannan buƙatu domin a kubutar da su cikin koshin lafiya.
Shi ma Manjo Janar Abubakar Rabe ya yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su ba tattaunawa dama, yana mai cewa akwai buƙatar samar da zaman lafiya da fahimtar juna domin kawo ƙarshen irin waɗannan matsaloli.
Abin da ya ja hankali shi ne cewa masu garkuwar ba su ambaci neman kuɗin fansa ba a cikin saƙon da suka isar ta bakin waɗanda suka sace, lamarin da ya bambanta da yawancin hare-haren garkuwa da mutane da ake samu a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa an tare motar tsohon janar ɗin ne tare da matarsa da direbansu a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli a ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina, inda aka yi awon gaba da su zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Lamarin ya sake tayar da hankali kan matsalar tsaro a yankunan arewa maso yammacin Najeriya, inda hare-haren masu garkuwa da mutane ke ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na daƙile ayyukansu.

0 Comments