Masana Sun Bayyana Dalilan Da Ke Hana Kama Masu Garkuwa da Mutane Ta Hanyar Wayoyi da TikTok

 

Yayin da matsalar sace mutane domin neman kuɗin fansa ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya, masana harkokin tsaro sun bayyana cewa akwai manyan ƙalubale da ke hana hukumomi amfani da bayanan wayoyi da kafafen sada zumunta wajen kamo masu laifin. 

A lokuta da dama, masu garkuwa da mutane kan shafe kwanaki ko ma watanni suna tattaunawa da iyalan waɗanda suka sace ta wayar tarho, suna neman kuɗin fansa. Haka kuma, wasu daga cikinsu kan bayyana a bidiyoyi da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta domin nuna ƙarfinsu ko kare kansu daga zarge-zarge.

Sai dai duk da waɗannan bayanai da suke fitowa fili, ba kasafai ake jin an kama waɗanda ake zargin ba ta hanyar amfani da fasahar sadarwa.

Ana Da Fasahar Amma Akwai Matsaloli

Masanin harkokin tsaro kuma shugaban wani kamfanin binciken tsaro, Kabiru Adamu, ya ce Najeriya na da damar amfani da fasahohin tattara bayanai daga intanet da wayoyin sadarwa domin gano masu laifi.

A cewarsa, abin da ake kira Open Source Intelligence (OSINT) ya zama muhimmin kayan aiki a ƙasashe da dama wajen bibiyar masu aikata laifuka da ƙungiyoyin ta’addanci.

Ya ce duk wani saƙo, bidiyo ko kiran waya da aka yi ta hanyar na'urorin zamani na iya samar da bayanan da za su taimaka wajen gano wanda ya aikata laifi idan aka yi amfani da dabarun da suka dace.

Rashin Haɗin Kai Tsakanin Sassa

Masanin ya bayyana cewa ɗaya daga cikin matsalolin da ke kawo tsaiko shi ne rashin cikakken haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani.

Ya ce akwai buƙatar a haɗa bayanan fasahar sadarwa cikin tsarin yaƙi da laifuka domin samun sakamako mai kyau.

A cewarsa, ƙasashe da dama sun riga sun rungumi irin wannan tsarin, yayin da Najeriya ke ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa shi.

Ƙalubalen Kayan Aiki da Intanet

Wani babban ƙalubalen kuma shi ne rashin isassun kayan aiki da za su ba jami’an tsaro damar kai dauki cikin sauri bayan gano inda masu laifi suke.

Haka kuma, yawancin manyan kafafen sada zumunta da kamfanonin intanet ba mallakin Najeriya ba ne, lamarin da ke sa samun bayanai ko umarni cikin gaggawa ya zama mai wahala.

Masana na cewa wannan matsala ba Najeriya kaɗai ta shafa ba, domin yawancin ƙasashen Afirka na fama da irin wannan ƙalubale wajen hulɗa da manyan kamfanonin fasahar duniya.

Kira Ga Gwamnati

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara saka hannun jari a fasahar tattara bayanai da horar da jami'an tsaro kan amfani da hanyoyin zamani wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane.

Sun ce amfani da bayanan wayoyi, kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa na zamani zai taimaka wajen rage ayyukan masu laifi da kuma inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

A halin yanzu dai, al'umma na ci gaba da tambayar ko za a iya amfani da fasahar da ake da ita domin kawo ƙarshen matsalar sace mutane da neman kuɗin fansa da ta zama babban ƙalubale ga tsaron Najeriya.

Post a Comment

0 Comments