Gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen dawo da fiye da 'yan ƙasarta 1,000 daga Afirka ta Kudu sakamakon ƙaruwar tashin hankali da hare-haren da ake dangantawa da ƙin jinin baƙi a wasu yankunan ƙasar.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce an fara tantance waɗanda suka nuna sha'awar komawa gida da raɗin kansu, yayin da hukumomin diflomasiyya ke aiki tare da gwamnatin Afirka ta Kudu domin sauƙaƙa tafiyar mutanen.
Mai magana da yawun ma'aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya bayyana cewa adadin masu neman komawa gida na ci gaba da ƙaruwa, amma ana sa ran zai haura mutum 1,000.
Fargabar ƙarin tashin hankali
Matakin ya zo ne bayan jerin zanga-zanga da tashe-tashen hankula da suka shafi baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu, lamarin da ya haifar da fargaba tsakanin dubban 'yan Afirka da ke zaune a ƙasar.
A cikin 'yan makonnin nan, ƙungiyoyin da ke adawa da baƙin haure sun ƙara matsin lamba kan gwamnati, suna neman a kori waɗanda ba su da takardun zama na doka.
Masana harkokin siyasa sun ce wannan yanayi ya sake tayar da muhawara kan matsalar rashin aikin yi, talauci da kuma yadda ake ɗora alhakin waɗannan matsaloli kan baƙi.
Najeriya da Ghana na ɗaukar mataki
Kafin wannan mataki na Najeriya, Ghana ta riga ta dawo da ɗaruruwan 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu, inda hukumomi suka bayyana cewa za a ci gaba da jigilar wasu ƙarin mutane idan buƙatar hakan ta taso.
Jakadancin Najeriya da ke Pretoria ya ce ya samu haɗin kai daga hukumomin Afirka ta Kudu domin ba wa masu laifukan shige da fice damar komawa gida cikin lumana maimakon tsare su.
Kiran zaman lafiya
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa baƙi tare da jaddada cewa ba za ta amince da ɗaukar doka a hannu ba.
Hukumomi sun kuma yi kira ga al'umma da su guji tayar da rikici, yayin da suke ƙoƙarin magance matsalar shige da fice da kuma damuwar tattalin arziki da ke addabar ƙasar.
Masu sa ido kan harkokin ci-rani sun bayyana cewa lamarin na nuna ƙalubalen da nahiyar Afirka ke fuskanta wajen tabbatar da 'yancin zirga-zirga da kariyar 'yan ƙasa a tsakanin ƙasashen nahiyar.

0 Comments