Rikicin Masarautar Kano: Ƙungiyar CSO ta nemi Tinubu ya gaggauta shiga tsakani, ta yi gargadin yiwuwar tashin hankali

Wata ƙungiyar haɗin gwiwar ƙungiyoyin fararen hula (CSO) ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta shiga tsakani kan rikicin Masarautar Kano, tana mai gargadin cewa rikicin na iya haifar da tashin hankali.

A cikin wata wasikar buɗe ido mai kwanan wata 8 ga Oktoba, 2026, wadda aka aika wa Shugaban Ƙasa, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta shiga tsakani cikin adalci, tare da ƙarfafa sa ido kan harkokin tsaro.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci a mutunta ayyukan shari'a da ake gudanarwa a gaban kotuna, tare da samar da tattaunawar zaman lafiya mai haɗa kowa da kowa, wadda za ta ƙunshi 'yan siyasa, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da shugabannin al'umma.

Wasikar ta samu sa hannun masu haɗa kan ƙungiyar guda uku, wato Hassan Ibrahim Gama, Mustapha Muhammed Chiroma da Peter Hassan Tijjani.

Ƙungiyar ta ce Kano ta kai wani matsayi mai matuƙar muhimmanci, sakamakon ci gaba da rashin jituwa da ke tattare da Masarautar Kano, kalaman jama'a da ake ganin za su iya ƙara rura wutar rikici, zarge-zargen tsoratar da abokan hamayyar siyasa, da kuma wasu abubuwan da suka faru kwanan nan da suka shafi kayan yaƙin neman zaɓe da tsaron jama'a.

Ta roƙi Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba ofishinsa, wajen ƙarfafa masu ruwa da tsaki su nuna kamewa, tare da hana waɗannan rikice-rikicen wuce gona da iri har su rikide zuwa tashin hankali.

Ƙungiyar ta jaddada buƙatar hankali, mutunta doka da tattaunawa mai ma'ana, domin samun hanyar warware matsalolin da ke tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa cikin lumana.

Post a Comment

0 Comments