FASHIN BAKI: Iran Ta Ce An Lalata ko An Lalata Jiragen Yaƙin Amurka 81

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi ikirarin cewa adadin jiragen saman sojin Amurka da aka lalata ko suka samu mummunar illa a yayin yaƙin da Iran ya kai 81, sama da adadin 42 da wani rahoton Majalisar Bincike ta Amurka (CRS) ya bayyana a watan Mayu.   

A wani saƙo da ya wallafa a X, Araghchi ya ce: “A watan Mayu, CRS ta amince cewa an lalata ko aka rasa jiragen sojin Amurka 42. Yanzu adadin ya kai 81.” Ya kuma yi ikirarin cewa ainihin barnar na iya fi wannan adadin yawa.

Menene rahoton CRS ya ce?

Muhimmin abu shi ne, rahoton CRS na ranar 5 ga Oktoba 2026 ya lissafa jiragen Amurka 81 da suka “ɓace ko suka lalace” (lost or damaged) tun bayan fara Operation Epic Fury a ranar 28 ga Fabrairu. Wannan ba yana nufin cewa dukkan jiragen 81 an harbe su ko an lalata su gaba ɗaya ba.

Rahoton ya haɗa da jiragen yaƙi, jiragen leƙen asiri, jiragen dakon mai da jiragen marasa matuƙi (drones), ciki har da F-15E, F-35A, KC-135 da MQ-9 Reaper.

Fashin baki

Saboda haka, ya dace a bambanta tsakanin “Iran ta lalata jirage 81” da kuma abin da rahoton CRS ya tabbatar: jiragen Amurka 81 sun yi hasara ko sun samu lalacewa bisa bayanan da aka tattara daga rahotannin kafafen yaɗa labarai, bayanan Ma'aikatar Tsaron Amurka da CENTCOM da kuma wasu bayanai daga Inspector General. CRS ta kuma nuna cewa adadin na iya sauyawa yayin da ake samun ƙarin bayanai.

Saboda haka, ikirarin Araghchi cewa “Iran ta lalata jiragen Amurka 81” ya fi ƙarfin abin da rahoton CRS ya tabbatar kai tsaye; rahoton ya yi magana ne kan jiragen da aka rasa ko suka lalace, ba wai duka an lalata su ta hanyar harin Iran ba.

Post a Comment

0 Comments