Ƙasashen Afirka Na Ci Gaba da Kwashe ‘Yan Kasarsu Daga Afirka ta Kudu Yayin Da Rikici Ke Ƙaruwa

 

Ƙasashe da dama na nahiyar Afirka sun ƙara kaimi wajen dawo da ‘yan ƙasarsu daga Afirka ta Kudu bayan sake ɓarkewar hare-hare da tashin hankali da suka shafi ‘yan ci-rani a wasu yankunan ƙasar. 

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 140, mafi yawansu ‘yan Malawi da Mozambique, sun fara komawa ƙasashensu ta hanyar motoci bayan sun shafe kwanaki suna neman mafaka a wani wurin taro da ke garin Kleinmond na lardin Western Cape.

Wadannan mutane na daga cikin daruruwan ‘yan ci-rani da aka kwashe daga gidajensu sakamakon rikice-rikicen da suka barke a yankin Overstrand, inda hukumomi suka samar musu da matsugunan wucin gadi domin kare lafiyarsu.

Gwamnatin Mozambique ta bayyana cewa ta karɓi sama da mutum 500 daga cikin ‘yan ƙasarta da suka dawo gida, yayin da Ghana ke ci gaba da shirye-shiryen dawo da ƙarin ‘yan ƙasarta bayan nasarar kwashe daruruwan mutane a makonnin baya.

A Najeriya kuwa, jami’ai sun ce sama da mutum 1,000 sun yi rajista domin komawa gida da son ransu, sakamakon fargabar tsaro da kuma yanayin rashin tabbas da ke ƙaruwa a wasu sassan Afirka ta Kudu.

Masu sa ido kan harkokin ƙaura sun bayyana cewa lamarin ya sake tayar da hankalin ƙasashen nahiyar, musamman ganin yadda ake samun ƙaruwar ƙiyayya da hare-hare kan baƙi a wasu lokuta a Afirka ta Kudu.

A martaninta, gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce za ta aika wakilai zuwa wasu ƙasashen Afirka domin tattauna halin da ake ciki tare da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen warware matsalar.

Sai dai wasu ƙungiyoyi masu adawa da kasancewar baƙi a ƙasar na ci gaba da matsa lamba ga gwamnati da ta tsaurara matakai kan ‘yan ci-rani, musamman waɗanda ba su da takardun izinin zama.

Masana na gargadin cewa idan ba a samu mafita mai ɗorewa ba, rikicin na iya yin tasiri ga dangantakar diflomasiyya tsakanin Afirka ta Kudu da wasu ƙasashen nahiyar, tare da ƙara jefa dubban mutane cikin mawuyacin hali.

Post a Comment

0 Comments